‘Yan bindiga sun kai hari ‘makarantar mata’ a Zamfara. – BBC News Hausa

289
Cheap web hosting in Nigeria

Wasu ‘Yan bindiga masu satar mutane sun kai hari a wata makarantar sakandare ta Mata a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

‘Yan bindigar sun kai harin ne a makarantar sakandare ta mata a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi da dare lokacin ake kallon wasan zakarun Turai, kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa BBC.

Ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta lokacin da suka shiga garin inda suka kashe wani mutum guda.

Wani dan sa-kai a garin na Moriki ya ce tun da la’asar ‘yan bindigar suka tare hanya kafin daga baya suka kawo hari da dare.

Ya ce sun tafi da wasu malamai biyu da wasu mata hudu masu dafawa dalibai abinci, amma ba su yi nasarar isa inda daliban ke bacci ba.

An sace surukin dogarin Buhari a Daura

An ware wa Zamfara naira biliyan 10 a kasafin kudin 2019

Satar mutane don kudin fansa a Zamfara na ci gaba da karuwa a baya-bayan nan, duk da yunkurin jami’an tsaro na kawo karshen matsalar da ta addabi yankin arewa maso yammaci.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

To Advertise or Publish a Story on NaijaLiveTv:
Kindly contact us @ Naijalivetv@gmail.com
Call or Whatsapp: 07035262029, 07016666694, 08129340000

Comments

comments